Posts

Chelsea: Hukumar Fifa za ta 'haramta' wa kungiyar sayen sabbin 'yan wasa

Image
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana fuskantar hukuncin dakatarwa daga sayen sabbin 'yan wasa, bayan wani bincike da hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta gudanar. Ana zargin kungiyar ne da sayen wasu 'yan wasa wadanda ba su kai shekara 18 da haihuwa ba. Wasu bayanai da aka samu daga shafin intanet na Football Leaks sun nuna cewa ana binciken kungiyar tsawon shekara uku a kan wasu 'yan wasa 19 da ta saya ciki har da Bertrand Traore. Shafin ya ce 14 daga cikin 'yan wasan 19 ba su cika shekara 18 a duniya ba.

An yi jana'izar Jamal Khashoggi a Masallacin Ka'aba da wasu sassam duniya

Image
Aranar Juma'a 16 ga watan Nuwamba ne daruruwan mutane suka taru don halartar jana'izar dan jaridar nan Jamal Khashoggi a masallacin Ka'aba da na Madina a kasar Saudia Arabia, da wasu biranen na duniya da suka hada da birnin Santambul, da Lonodn, da Paris, da Washington. An kashe shi ne a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyyan ba tare da an gano gawarsa ba, kuma har yanzu ba a gano gawarsa ba. Shugaba Reccep Erdogan yana zargin gwamnatin Saudiyya da kisan, sai dai kasar ta musanta, amma hukumomin na Saudiya sun ce za su hukunta jam'ian tsaron kasar da suka kashe Jamal.

EFCC ta gargadi 'yan canjin kudi a Najeriya

Image
Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati Ibrahim Magu ya gargadi masu canji kudi da su daina taimaka wa harkokin cin hanci da rashawa da wadansu 'yan siyasa suke yi a kasar. Shugaban ya ce hukumar za ta gurfanar da duk wani dan siyasa ko banki da aka samu laifin taka dokokin hada-hadar kudi a kasar, kamar yadda aka bayyana a wata sanarwa da hukumar ta aike wa BBC.

Wayne Rooney ne zai yi wa Ingila kyaftin a wasansa na karshe

Image
D Rooney, wanda yanzu yake wasa a kungiyar DC United da ke Amurka, ya yi ritaya ne bayan ya yi wa kasarsa wasanni 199, inda ya zura kwallaye 53. Sai dai hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA) ta bukaci dan kwallon ya dawo ya taka wa kasarsa leda a wasan saboda a martaba shi don bajintar da ya nuna lokacin da yake wakiltar kasarsa a wasan kwallon kafa. Wasan ne kuma zai zama wasan da zai yi wa Ingila na karshe, abin da zai sa ba zai buga wasan da kasar za ta yi da Kuroshiya ba a gasar Nations League a ranar Lahadi mai zuwa.Rooney, wanda yanzu yake wasa a kungiyar DC United da ke Amurka, ya yi ritaya ne bayan ya yi wa kasarsa wasanni 199, inda ya zura kwallaye 53. Sai dai hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA) ta bukaci dan kwallon ya dawo ya taka wa kasarsa leda a wasan saboda a martaba shi don bajintar da ya nuna lokacin da yake wakiltar kasarsa a wasan kwallon kafa. Wasan ne kuma zai zama wasan da zai yi wa Ingila na karshe, abin da zai sa ba zai buga wasan da kasar za ta yi da Kuroshiya

Dr Ahmad Gumi: El-Rufai ya yi kuskure da ya zabi Musulma mataimakiya

Image
Sanannen malamin nan na addinin Islama Sheikh Ahmad Gumi, ya soki shawarar da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El- Rufai ya yanke na daukar mace a matsayin mataimakiya a zabe mai zuwa. Dr Gumi ya bayyana ra'ayinsa ne a yayin da gwamnan El-Rufai ya shaidawa wani taro na mabiya addinin kirista daga kudancin jihar Kaduna cewa babu batun addini ko kabilanci a zabin da yayi na musulma a matsayin mataimakiyarsa. Gwamnan na Kaduna ya zabi Dr Hadiza Balarabe a matsayin wadda za ta gaji Barnabas Bala Bantex wanda ke taimaka masa tun 2015. Mista Bantex kirista ne kuma zai ajiye mukamin mataimakin gwamna ne saboda ya sami damar tsayawa takarar sanata.

Jami'an tsaron Najeriya sun binciki Abubakar Atiku

Image
F Dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP mai hamayya, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa jami'an tsaron kasar sun bincike shi ranar Lahadi jim kadan da isarsa Abuja, babban birnin tarayyar kasar. Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya koma kasar ne daga birnin Dubai inda ya shafe kwana da kwanaki tare da wasu abokan siyasa da mukarrabansa. Bai yi karin bayani kan dalilin da ya sa aka bincike shi,  Kawo lokacin wallafa wannan labarin hukumomi ba su ce uffan ba. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce jami'an tsaron sun dauki matakin ne da zummar yi masa barazana.