Posts

Showing posts from November, 2018
Image
http://www.Arewafashions.blogspot.com.ng/2018/11/shirye-shiryen-zaben-najeriya-anfara.html

Chelsea: Hukumar Fifa za ta 'haramta' wa kungiyar sayen sabbin 'yan wasa

Image
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana fuskantar hukuncin dakatarwa daga sayen sabbin 'yan wasa, bayan wani bincike da hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta gudanar. Ana zargin kungiyar ne da sayen wasu 'yan wasa wadanda ba su kai shekara 18 da haihuwa ba. Wasu bayanai da aka samu daga shafin intanet na Football Leaks sun nuna cewa ana binciken kungiyar tsawon shekara uku a kan wasu 'yan wasa 19 da ta saya ciki har da Bertrand Traore. Shafin ya ce 14 daga cikin 'yan wasan 19 ba su cika shekara 18 a duniya ba.

An yi jana'izar Jamal Khashoggi a Masallacin Ka'aba da wasu sassam duniya

Image
Aranar Juma'a 16 ga watan Nuwamba ne daruruwan mutane suka taru don halartar jana'izar dan jaridar nan Jamal Khashoggi a masallacin Ka'aba da na Madina a kasar Saudia Arabia, da wasu biranen na duniya da suka hada da birnin Santambul, da Lonodn, da Paris, da Washington. An kashe shi ne a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyyan ba tare da an gano gawarsa ba, kuma har yanzu ba a gano gawarsa ba. Shugaba Reccep Erdogan yana zargin gwamnatin Saudiyya da kisan, sai dai kasar ta musanta, amma hukumomin na Saudiya sun ce za su hukunta jam'ian tsaron kasar da suka kashe Jamal.

EFCC ta gargadi 'yan canjin kudi a Najeriya

Image
Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati Ibrahim Magu ya gargadi masu canji kudi da su daina taimaka wa harkokin cin hanci da rashawa da wadansu 'yan siyasa suke yi a kasar. Shugaban ya ce hukumar za ta gurfanar da duk wani dan siyasa ko banki da aka samu laifin taka dokokin hada-hadar kudi a kasar, kamar yadda aka bayyana a wata sanarwa da hukumar ta aike wa BBC.

Wayne Rooney ne zai yi wa Ingila kyaftin a wasansa na karshe

Image
D Rooney, wanda yanzu yake wasa a kungiyar DC United da ke Amurka, ya yi ritaya ne bayan ya yi wa kasarsa wasanni 199, inda ya zura kwallaye 53. Sai dai hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA) ta bukaci dan kwallon ya dawo ya taka wa kasarsa leda a wasan saboda a martaba shi don bajintar da ya nuna lokacin da yake wakiltar kasarsa a wasan kwallon kafa. Wasan ne kuma zai zama wasan da zai yi wa Ingila na karshe, abin da zai sa ba zai buga wasan da kasar za ta yi da Kuroshiya ba a gasar Nations League a ranar Lahadi mai zuwa.Rooney, wanda yanzu yake wasa a kungiyar DC United da ke Amurka, ya yi ritaya ne bayan ya yi wa kasarsa wasanni 199, inda ya zura kwallaye 53. Sai dai hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA) ta bukaci dan kwallon ya dawo ya taka wa kasarsa leda a wasan saboda a martaba shi don bajintar da ya nuna lokacin da yake wakiltar kasarsa a wasan kwallon kafa. Wasan ne kuma zai zama wasan da zai yi wa Ingila na karshe, abin da zai sa ba zai buga wasan da kasar za ta yi da Kuroshiya

Dr Ahmad Gumi: El-Rufai ya yi kuskure da ya zabi Musulma mataimakiya

Image
Sanannen malamin nan na addinin Islama Sheikh Ahmad Gumi, ya soki shawarar da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El- Rufai ya yanke na daukar mace a matsayin mataimakiya a zabe mai zuwa. Dr Gumi ya bayyana ra'ayinsa ne a yayin da gwamnan El-Rufai ya shaidawa wani taro na mabiya addinin kirista daga kudancin jihar Kaduna cewa babu batun addini ko kabilanci a zabin da yayi na musulma a matsayin mataimakiyarsa. Gwamnan na Kaduna ya zabi Dr Hadiza Balarabe a matsayin wadda za ta gaji Barnabas Bala Bantex wanda ke taimaka masa tun 2015. Mista Bantex kirista ne kuma zai ajiye mukamin mataimakin gwamna ne saboda ya sami damar tsayawa takarar sanata.

Jami'an tsaron Najeriya sun binciki Abubakar Atiku

Image
F Dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP mai hamayya, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa jami'an tsaron kasar sun bincike shi ranar Lahadi jim kadan da isarsa Abuja, babban birnin tarayyar kasar. Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya koma kasar ne daga birnin Dubai inda ya shafe kwana da kwanaki tare da wasu abokan siyasa da mukarrabansa. Bai yi karin bayani kan dalilin da ya sa aka bincike shi,  Kawo lokacin wallafa wannan labarin hukumomi ba su ce uffan ba. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce jami'an tsaron sun dauki matakin ne da zummar yi masa barazana.

An sace 'Yan makaranta 81 a yammacin kamaru

Image
An sace mutane da dama, cikin su harda yara a wata makaranta dake BIrnin Bamenda na jamhuriyar kamaru. Kamfanonin dillacin labarai sun ambato wasu majiyoyj na gwamnatin Da sojojin kasar da Ba sa so a bayyana sunayensu sunce an sa CE Akalla mutum 79. Majiyoyi sun bayyana wa manema labarai cewa "Yan bindiga ne suka Sace mutanen ranar litinin da safe.  Dama dai yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin Kamaru na fama da rikice-rikicen 'Yan aware na baya bayan nan.

Atiku da Buhari: shin matasan Najeriya sun Gaza ne?

Image
Rahotannin da muke Kawo muku Daga  'Yan jaridar africa, a wannan karon Babban editan dailytrust fake Najeriya, munnir Dan Ali Yayi mana nazari Kan dalilan da suka sanya kasar da fiye da rabin mazaunanta 'Yan kasar Da shekara 35 ne, ta tsayar da tsofaffi domin yi mata takara  a zaben da Za ayi Badi. Ranar da za'a gudanar da zabe mai zuwa, dukkan manyan 'Yan takarar Shugabancin Najeriya biyu, shugaba Muhammadu Buhari da takwaransa Na Babban jam'iyar hamayya ta Atiku Abubakar zasukai shekara 148 a Jumlace. Hakan tamkar wani arashi ne idan akwai la'akari da guguwar datatasko Lokacin da aka sanya Hannu kan dokar rage shekarun tsayawa takara Kan mukamai daban daban a kasar, Wanda akwai wa lakabi " "Not too young to run" inda yazama maison yin takararshugabancin Kasa sai ya kasance dan shekara 30-35 kamar yadda yake abaya.

kukalli zafafan hotunan jarumar kannywood , wato fitacciyar jaruma "Maryam Yahya"

Image
Like and share Wanda yai posting: h fashion @ Arewafashions.blogspot. ccom

Mutane 50 aka kashe a rikicin 'Yan Shi'a a Abuja "Burtaniya"

Image
Burtaniya tace mutum 50 aka kashe a arangamar da akayi tsakanin 'Yan Shi'a da jami'an tsaron Najeriya a Abuja makon jiya. Kungiyar 'Yan Shi'a mabiya sheikh Ibrahim El zakzaky tace an kashe Mambobinta fiye da 50.koda yake rundunar sojin kasar tace mutum Uku ne kawai suka mutu a rikicin. Sanarwar da wata mai magana da yawun ofishin jakadancin Burtaniya na Najeriya Louise Edwards ta aikawa manema Labarai ranar lahadi, cewar kasarta ta bayyanawa gwamnatin Najeriya mutukar damuwa kan rikicin da kuma damuwa kan Mutanen da aka kashe sakamakonsa. Sanarwa ta bukaci dakarun tsaron Najeriya su dinga gudanar Da ayyukansu bisa dokokin kasashen duniya Dana cikin gida Da kuma kare hakkin farar hula.

Anyi jana'izar janar Idris Alkali a Abuja.

Image
Anyi jana'izar janar Idris Alkali mai ritaya a Abuja, Babban birnin Tarayyar Najeriya ranar Asabar da rana. Mutane da dama ne, ciki har da babban hafsan sojin Najeriya Janar Yusif Buratai, suka halacci jana'izar janar din, Wanda Aka kashe a jahar filato dake arewa ta tsakiyar kasar a Satan Satumba. A ranar laraba ne sojin kasar ta gano gawar janar din A wata rijiya da ke gushwet a gundumar shen ta karamar Hukumar jos south a jihar filato. Kwamandan runduna ta uku ta dakarun kasar, Birgediya Janar umar Muhammed yace daya Daga cikin Wanda Suka mika Kansu ga 'Yan sanda ne ya nunawa sojoji Rijiyar, wadda ba'a amfani da iya.

Rikicin 'Yan Shi'a:: sojoji sun kafa hujja da Trump kan Harbin 'Yan Shi'a.

Image
Rundunar sojin Najeriya ta kafa hujja kan budewa 'Yan Shi'a Wuta, da wani fefen bidiyo na shugaban kasar Amurka Donald Trump, Wanda a ciki yake cewa  sojoji zasu iya Amfani da baki 'yan ci rani dake jifansu da duwatsu. "Idan sukayi jifa da duwatsu..... Ku dauka sunyi da bindiga ne" Inji mista Trump a wani fefen bidiyo. Jami'an tsaron Najeriya sunkama mabiya Shi'a 400 bayan Mummunan artabu na tsahon kwanaki a Abuja.

kukalli zafafan hotunan jarumar kannywood "hafsa Idris wadda akafi sani da Barauniya.

Image
Like      and       share Wanda yai posting : h fashion